28 Satumba 2019 - 04:39
Jirgin Ruwan Birtaniya Da Iran Ke Tsare Da Shi Ya Kama Hanyar Dubai A Yau

Katafaren jirgin ruwan dakon main a kasar Birtanya da Iran ta kame kuma ta tsare shin a tsawon watanni biyu ya bar kasar ta Iran a yau bayan sakinsa.

(ABNA24.com) Katafaren jirgin ruwan dakon main a kasar Birtanya da Iran ta kame kuma ta tsare shin a tsawon watanni biyu ya bar kasar ta Iran a yau bayan sakinsa.

Tashar presstv ta bayar da rahoton cewa, hukumar kula da harkokin zirga-zirgar jiragen ruwa ta kasar Iran ta sanar da cewa, da misalign karfe 9 na safiyr yau Juma’a jirgin na Birtaniya Stena Impero ya bar gabar ruwan Bandar Abbas da ke yammacin kasar Iran, inda ya kama hanyarsa zuwa gabar ruwa ta birnin Dubai.

Tun a ranar 19 ga watan Yulin da ya gabata ne dai jami’an tsaron kasar Iran suka kame katafaren jirgin dakon man na Birtaniya a cikin tekun Oman, bayan da ya saa ka’idojin zirga-zirgar jiragen ruwa a cikin tekun, daga ciki kuwa har kashe fitilunsa, da kuma kashe na’urar tantance taswira ta GPS.

Iran ta tsare jirgin an Birtaniya sawon fiye da watanni biyu, tare da gudanar da bincike, ida daga karshe kotun koli ta kasar Iran din ta bayar da umarnin sakin jirgin da yake dauke da danyen man fetur na kasar Birtaniya.




/129